Isa ga babban shafi

An rantsar da shugaban gwamnatin sojin Gabon na rikon kwarya

A yau litinin ne aka rantsar da Janar din da zai jagoranci Gabon a matsayin shugaban rikon kwarya, bayan juyin mulkin kasar a makon da ya gabata, inda zai rike ikon kasar na wani lokaci da ba a bayyana ba bayan hambarar da daular Bongo na kasar shekaru 55.

Janar Brice Oligui Nguema
Janar Brice Oligui Nguema © AFP
Talla

Janar Brice Oligui Nguema, ya jagoranci juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar Larabar da ta gabata kan shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, wanda ya fito daga gidan iyalan da suka mulki kasar sama da shekaru hamsin.

Korar ta zo ne bayan da aka ayyana Bongo mai shekaru 64 a matsayin wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan da ya gabata bayan da ‘yan adawa suka bayyana zargin cewa an tafka magudi.

Jagororin juyin mulkin sun ce sun rusa hukumomin kasar, sun soke sakamakon zaben, da kuma rufe iyakokin kasar, inda daga bisani suka ce sun yanke shawarar bude su.

Kasashen dai ba su amince da Oligui a matsayin halastaccen shugaban kasar Gabon ba, wanda yanzu haka ke fuskantar matsin lamba kan ya bayyana shirinsa na maido da mulkin farar hula.

Sabon shugaban gwamnatin mulkin sojin dai, ya sha nanata alkawarin da ya yi na shirya zabuka cikin 'yanci da lumana, ba tare da bayyana lokacin da za a yi ba amma ya ce sai an fara aiwatar da sabon kundin tsarin mulki ta hanyar kuri'ar raba gardama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.