Isa ga babban shafi

Sojojin da suka yi juyin mulki a Gabon sun sanar da bude iyakokin kasar

Sojojin da suka hambarar da Ali Bongo Ondimba da ya kwashe sama da shekaru 14 yana mulkin Gabo, sun sanar cewa za su sake bude iyakokin kasar daga wannan Asabar, wanda zai fara aiki nan take, kwanaki uku bayan rufe su.

Huton shugabannin sojin Gabon yayin sanar da shirin bude kan iyaka. 2/09/23
Huton shugabannin sojin Gabon yayin sanar da shirin bude kan iyaka. 2/09/23 AFP - -
Talla

Sanarwar bude kan iyakon na sama da kasa da na ruwa na zuwa ne kwanaki biyu gabanin rantsar Janar Brice Oligui Nguema amatsayin shugaban kasar na rikon kwarya ba tare da bayyana wani wa’adi da zai yi ba a madafun iko kafin shirya zabe.

A ranar Jumma’ar da ta gabata Shugaban sojin ya yi alkawarin samar da sabon kundin tsarin mulki Gabon da sabon kundin zabe, lamarin da ke zama tamkar murna ke komawa ciki ga manyan jam'iyyun adawar da suka bukaci ya mayar da mulki ga farar hula ta hanyar mika shi ga Albert Ondo Ossa, wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na ranar 26 ga watan Agusta.

Sojoji sun sanar da karbe mulki ne kasa da mintuna sittin bayan da hukumar zaben kasar ta ayyana shugaban kasar Ali Bongo Ondimba, amatsayin wanda ya nasara tun a zagayen farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.