Isa ga babban shafi

Jagoran 'yan adawar Gabon ya bayyana juyin mulkin da aka yi a matsayin hadin baki

Yayin da jama'a a Gabon ke murnar juyin mulkin ranar Laraba, jagoran 'yan adawar kasar ya ce al'amura ba su canza ba.

Jagoran 'yan adawar Gabon kenan, Albert Ondo Ossa.
Jagoran 'yan adawar Gabon kenan, Albert Ondo Ossa. AFP - STEEVE JORDAN
Talla

Sojoji sun kwace mulki sa'o'i kadan bayan an sanar da hambararren shugaban kasar Ali Bongo a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa.

Sai dai a wata hira da kafar yada labaran Faransa, TV5 Monde a ranar Alhamis Albert Ondo Ossa, ya bayyana juyin mulkin a matsayin al'amari na hadin baki tsakanin wasu iyalai guda, da nufin cewa su kadai ne za su ci gaba da rikon mulkin kasar.

Kalaman nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da sojoji suka karbe mulki inda suka jefa Bongo a gidan yari, bisa zargin shi da rashin gudanar da mulki wanda ya jefa kasar cikin rudani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.