Isa ga babban shafi

Jagoran adawa a Gabon ya roki Sojoji su kammala kirga kuri'un zaben kasar

Jagoran adawa a Gabon Albert Ondo Ossa da ke ikirarin nasara a zaben da Sojoji suka rusa bayan juyin mulki, ya roki sojojin da ke jan ragamar kasar da su kammala kirgen kuri’un da aka kada a zaben kasar.

Mr Albert Ondo Ossa,dan takarar jam'iyyar adawa a Gabon.
Mr Albert Ondo Ossa,dan takarar jam'iyyar adawa a Gabon. AFP - STEEVE JORDAN
Talla

A wani jawabi da ya gabatar, Mr Ossa ya godewa Sojojin kan tseratar da Gabon daga kama karya da kuma yunkurin sauya sakamakon zabe, sai dai ya ce akwai bukatar kammala kirgen kuri’un da al’ummar kasar suka kada.

Mr Ossa wanda tun gabanin sanar da sakamakon zabe ya bayyana kansa a matsayin wanda ya yi nasara, ya ce juyin mulkin Sojin ya bai wa jam’iyyar adawar gwarin gwiwar samun adalci a zaben.

Jim kadan bayan sanar da sakamakon zaben da ke bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe ne sojoji suka sanar da juyin mulki bayan zargin magudin da ya dabaibaye zaben.

Sakamakon da hukumar zaben Gabon ta fitar dai ya nuna cewa Bongo ya lashe kashi 64.27 na yawan kuri’un da aka kada yayin Mr Ossa na jam’iyyar adawa ya lashe kashi 30.77.

A cewar Mr Ossa hada kai da Sojojin da suka yi juyin mulkin zai samar da mafita ga al’ummar Gabon wadanda ke fuskantar matsin rayuwa karkashin mulkin Bongo wanda iyalan gidansu suka shafe gomman shekaru su na mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.