Isa ga babban shafi

Rasha ta hana a lafta wa sojojin Mali takunkumai

Majalisar Dinkin Duniya za ta kawo karshen takunkuman da ta lafta wa Mali bayan Rasha ta hau kujerar na ki domin hana sabunta takunkuman kan gwamnatin sojin kasar.

Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Mali. AP
Talla

An lafta wa Mali takunkumai ne don ladabtar da duk wanda ke da hannu wajen hana yarjejeniyar zaman lafiya ta shekarar 2015 aiki, tare da hana isar  da kayayyakin agaji cikin kasar, baya ga aikata laifukan take hakkin bil’adama da kuma jefa kananan yara cikin aikin soji.

A cikin wannan watan ne, masu sanya ido kan takunkuman Majalisar Dinkin Duniya a Mali suka bayar da rahoton cewa, dakarun Mali da abokan huldarsu  na ketare ta fannin tsaro na yada ta’addanci ta hanyar cin zarafin mata tare da take hakkokin bil’adama.

An dai ce, wadannan abokan huldar Mali ba kowa ba ne face mayakan Wagner na Rasha.

Mambobi 13 na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun kada kuri’ar amincewa da kudirin da Faransa da Hadaddiyar Daular Larabawa suka gabatar domin fadada takunkumai kan kasar Mali.

Sojojin haya na Wagner na Rasha a Mali.
Sojojin haya na Wagner na Rasha a Mali. © RFI

Sai dai Rasha ta hau kujerar na ki, yayin da Chile ta kaurace wa kada kuri’ar baki daya.

 

A maimakon haka, Rasha ta dage kan cewa, sai dai a lafta wa Mali takunkumai na karshe kuma na tsawon shekara guda kacal, wanda daga nan ba za a sake kakaba mata takunkumai ba. Amma dai ba ta samu goyon bayan kasashen na Kwamitin Tsaron ba.

A farkon watan Agusta ne, sojojin Mali suka rubuta wa Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wata wasika, inda a cikinta suka bukaci a janye takunkuman da aka kakaba wa kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.