Kamfanin 3M zai biya diyya ga sojojin Amurka da suka kurumce
Babban Kamfanin Kere-keren kayayyakin fasaha na 3M ya amince ya biya dala biliyan 6 ga tsoffin sojojin Amurka da suka zarge shi da sayar musu da lalataccen iyapis da ya haddasa musu kurumcewa a cewarsu.
Wallafawa ranar:
Kamfanin na fatan wannan yarjejeniya ta biyan makuden kudaden ga tsoffin sojojin za ta kawo karshen dadaddiyar shari’ar da ake yi kan batun.
Dubban tsoffin sojojin na Amurka ne suka shigar da karar kamfanin a kotu, inda suka yi korafi kan cewa, sun kurumce sakamakon amfani da iyapis din da kamfanin na 3M ya kera.
Wannan yarjejeniyar da aka cimma ta kunshi cewa, kamfanin zai biya jumullar dala biliyan 6 tsakanin shekarar 2023 zuwa 2029, inda zai biya dala biliyan 5 cikin tsabar kudi, sannan ya biya sauran biliyan 1 ta hanyar sayar wa sojojin da hannayen jari kamar yadda 3M din ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kamfanin ya sayar wa sojojin da iyapis din ne tsakanin shekarar 2003 zuwa 2015, yayin da ya dage kan cewa, hajarsa ba ta da wata matsala muddin aka yi amfani da ita yadda ya dace.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu