Isa ga babban shafi

Gwamnatin Libya za ta bincike ministar da ta gana da Isra'ila

Firaministan Libya da ke samun goyon bayan kasashen duniya ya dakatar da babbar jami’ar diflomasiyarsa bayan ta gana da takwaranta na Isra’ila, lamarin da ya haifar da zanga-zanga a kasar da ke adawa da Isra’ila.

Najla Mangoush
Najla Mangoush AP - Darko Vojinovic
Talla

Libya mai arzikin man fetur da ta fada cikin rikici bayan mutuwar tsohon shugabanta Mo’ammar Gaddafi, ta rabu gida biyu tun shekarar 2014, inda bangaren gwamnatin firaminista Abdelhamid Dbeibah ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya a birnin Tripoli, yayin da dayan bangaren ‘yan adawa ke mulki a gabashin kasar.

A cikin daren ranar Lahadi ne, fusatattun matasa suka yi zanga-zanga a babban birnin Libya da sassan wasu biranen kasar, inda suka toshe hanyoyi tare da kone-konen tayoyi, ga kuma tutocin falasdinu a hannayensu.

Sun gudanar da wannan zanga-zangar ce jim kadan da samun  labarin cewa, Najla al-Mangoush ta gana da takwaranta na Isra’ila a birnin Rome a makon jiya.

Yanzu haka an dakatar da Mangoush, sannan za a kaddamar da bincike a kanta kamar yadda gwamnatin Dbeibah ta sanar bayan ‘yan sa’o’i da sanarwar da ta fito daga Ministan Harkokin Wajen Isra’ila, Eli Cohen da ke cewa, lallai ya yi ganawa mai armashi da Mongoush.

A wannan Litinin din ne, Hukumar Tsaron Cikin Gidan Libya ta ce, babu wanda ya bai wa Mangoush izinin ficewa daga kasar da ke arewacin Afrika bayan rahotannin da suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta na cewa, ta yi balaguro zuwa Turkiya a cikin dare a daidai lokacin da zanga-zangar ta tsananta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.