Isa ga babban shafi

Labarin matsalar sauyin yanayi a duniya cikin hotuna

Sauyin yanayi na ci gaba da haddasa ibtila'o'i masu yawa a sassan duniya tare da lakume dimbin rayuka a daidai lokacin da masana ke gargadin cewa, wajibi ne a dauki matakin kare muhalli muddin dan adam na son rayuwa cikin salama a doran wannan duniyar da muke ciki.

Wani jirgi mai saukar ungulu na shawagi a gabar teku bayan faduwar rana a daidai lokacin da guguwar Hilary ke dosar Del Mar a California na Amurka.
Wani jirgi mai saukar ungulu na shawagi a gabar teku bayan faduwar rana a daidai lokacin da guguwar Hilary ke dosar Del Mar a California na Amurka. REUTERS - MIKE BLAKE
Talla

 

Wasu ma'aurata kenan da ke hanyar komawa gidansu da suka kaurace masa sakamakon ibtila'in wutar daji a Canada. Hayaki ne ya turnike hatta sararin samaniyar kogin.
Wasu ma'aurata kenan da ke hanyar komawa gidansu da suka kaurace masa sakamakon ibtila'in wutar daji a Canada. Hayaki ne ya turnike hatta sararin samaniyar kogin. AP - Darryl Dyck
Wasu mazauna Hawaii kenan da suka tsira daga gagarumin ibtila'in wutar daji a Amurka
Wasu mazauna Hawaii kenan da suka tsira daga gagarumin ibtila'in wutar daji a Amurka AP - Jae C. Hong
Yadda wutar daji ta yi wa gine-gine illa a Lahaina da ke Hawaii na Amurka
Yadda wutar daji ta yi wa gine-gine illa a Lahaina da ke Hawaii na Amurka AP - Jae C. Hong
Wani mutun na shan hasken rana bayan ya yi wanka a kogi sakamakon tsananin zafi a Marseille da ke kudancin Faransa.
Wani mutun na shan hasken rana bayan ya yi wanka a kogi sakamakon tsananin zafi a Marseille da ke kudancin Faransa. AP - Daniel Cole
Yadda ake hango wuta a saman tsaunuka kusa da wasu gidajen da jama'a suka kaurace musu a kauyukansu da ke tsibirin Canary a Spain.
Yadda ake hango wuta a saman tsaunuka kusa da wasu gidajen da jama'a suka kaurace musu a kauyukansu da ke tsibirin Canary a Spain. REUTERS - NACHO DOCE
Wata mota na ratsawa ta cikin ruwa a daidai lokacin da guguwar Hilary ta doshi birnin Palm Springs a California na Amurka
Wata mota na ratsawa ta cikin ruwa a daidai lokacin da guguwar Hilary ta doshi birnin Palm Springs a California na Amurka REUTERS - BRYAN WOOLSTON
Yadda hayaki ke ratsowa ta saman Tafkin Okanagan daga Kelowna da ke British Columbia.
Yadda hayaki ke ratsowa ta saman Tafkin Okanagan daga Kelowna da ke British Columbia. AP - Joe O'Connal
Wani jami'in kashe gobara na ratsawa ta cikin hayakin wutar da ta shi a kan tsauni a Soacha da ke kusa da Bogota a Colombia.
Wani jami'in kashe gobara na ratsawa ta cikin hayakin wutar da ta shi a kan tsauni a Soacha da ke kusa da Bogota a Colombia. AP - Fernando Vergara

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.