Isa ga babban shafi

Sai nan da shekara uku za mu mika mulki ga farar hula a Nijar - Tchiani

Shugaban gwamnatin sojan Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya ce sojojin kasar za su mika mulki ga gwamnatin farar hula nan da shekaru uku masu zuwa.

Janar Abdourahmane Tchiani lokacin da yake gabatar da jawabi ta kafat talibijin, ranar 28 ga watan Yuli, 2023, bayan hambarar da zababben shugaban kasar Muhammad Bazoum.
Janar Abdourahmane Tchiani lokacin da yake gabatar da jawabi ta kafat talibijin, ranar 28 ga watan Yuli, 2023, bayan hambarar da zababben shugaban kasar Muhammad Bazoum. AP
Talla

Janar din ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da aka yada a gidan talabijin din kasar a daren ranar Asabar.

Tchiani ya bayyana hakan ne bayan ganawa da tawagar kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS karkashin jagorancin tsohon shugaban Najeriya Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.

Janar Tchiani ya ce nan da wata guda, gwamnatin mulkin soji za ta kafa wani kwamiti da zai yi nazari tare da kafa sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Yayin da ya ci gaba da cewa Nijar ba ta son shiga yaki, inda ya ce karamar kasar za ta kare kanta idan bukatar hakan ta taso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.