Isa ga babban shafi

Rasha ta sanyawa mai shigar da kara na ICC da wasu ministocin Birtaniya takunkumi

Kasar Rasha ta sanar da kakaba takunkumi kan mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wanda ke neman a kama shugaba Vladimir Putin, da kuma ministocin Birtaniyya da suka yi kakkausar suka ga harin gwamnatin Moscow a Ukraine.

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan via REUTERS - SPUTNIK
Talla

Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta yi Allah-wadai da tallafin soji da aka samu daga birnin Landan zuwa Kyiv da kuma yadda ake aiwatar da mugun nufi na adawa da Rasha, bayan shafe kusan shekara guda da rabi ana yaki a Ukraine.

Alkalin kotun ICC, Karim Khan, wanda dan Birtaniya ne, ya bayar da sammacin kama Putin a watan Maris kan zargin korar yaran da suka fito daga Ukraine ba bisa ka'ida ba.

Rasha, wacce ba mamba bace a kotun ta ICC, ta dage kan sammacin da aka yi wa Putin a matsayin bita da kulli.

Kimanin mutane 54 ne Rasha ta saka cikin jerin takunkumin da Rasha ta kakabawa ‘yan Birtaniyya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.