Isa ga babban shafi

Akwai fargaba a barazanar Rasha game da yiwuwar kai mana hari -ICC

Kotun hukunta manyan laifuka ta ICC ta bayyana matukar damuwa game da barazanar da Rasha ta yi mata kan yiwuwar kai mata hari da makami mai linzami don mayar da martini kan sammacin da ta bayar na kamo shugaba Vladimir Putin kan zarginsa da aikata laifukan yaki.

Zauren kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC.
Zauren kotun hukunta manyan laifuka ta Duniya ICC. © ICC-CPI
Talla

Sanarwar da ICC ta fitar ta ce akwai fargaba kan kalaman tsohon shugaban Rasha Dmitry Medvedev wanda ya yi barazanar farmakar ginin kotun da ke birnin Hague ta hanyar harba mata makamaki mai linzami da ke cin dogon zango.

ICC ta ce Rashan ta kuma yi barazana ga shugaban kotun Karim Khan da sauran alkalan da ke dakon jagorantar shari’ar ta Putin kan zargin aikata laifukan yaki.

Majalisar gudanarwar kotun ta nanata cewa daukar matakin farmakar ta ko jami’anta babban zunubi ne da ya sabawa dukkanin dokokin kasa da kasa.

A cewar kotun abin tir ne lura da yadda Rasha ta iya furta irin wannan kalamai na yiwuwar kai hari da makami mai linzami kan kotun ta Duniya.

Majalisar a zaman da ta yi, ta goyi bayan matakin ICC na bayar da sammacin kamen ga Putin don amsa tuhuma kan zarge-zargen da ke kansa na aikata laifukan yaki ciki har da kwashe tarin kananan yara daga Ukraine zuwa Rasha.

A litinin din makon nan ne, tsohon shugaban na Rasha Dmitry Medvedev ya bayyana cewa abu ne mai yiwuwa a iya harba makami mai linzami daga cikin jirgin yakin Rasha da ke kan tekun North Sea zuwa ginin kotun ICC da ke birnin Hague.

A cewarsa kowa na tafiya ne karkashin ikon All… yayinda makamai masu linzami ke keta sararin samaniya don haka idan ana tafiya a rika ankarewa da sararin samaninya cikin nutsuwa da kamala.

A juma’ar makon jiya ne ICC ta fitar da sammacin kame shugaba Vladimir Putin saboda karya ka’idar da ya yi wajen kwashe tarin kananan yara daga yankin da ya mamaye a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.