Isa ga babban shafi

Kotun ICC ta bayar da sammacin kama shugaba Putin na Rasha

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa, ICC ta bayar da sammacin kamo mata shugaban Rasha Vladimir Putin saboda haramtaccen matakin da ya dauka na tasa keyar kananan yaran Ukraine zuwa gida.

Shugaban Rasha Vladimir Putin
Shugaban Rasha Vladimir Putin AP - Dmitry Astakhov
Talla

Kotun ta ICC mai cibiya a birnin Hague ta ce, ta kuma bayar da wani sammacin kama Kwamishiniyar Kare Hakkin Yara na Fadar Shugaban Rasha, Maria Lvova-Belova saboda zargin ta da hannu wajen tasa keyar kanana yaran.

Sai dai Rasha ba ta cikin mambobin ICC, abin da ya haifar da sarkakiya kan yadda kotun za ta matsa kaimi kan sammacin.

Tuni gwamnatin Rasha ta mayar da martani, tana bayyana wannan matakin na kotun ICC a matsayin shirme.

Ita kuwa gwamnatin Ukraine ta yi jinjina ne ga kotun ta ICC, tana mai bayyana matakinta a matsayin wani sabon tarihi da aka kafa a tsarin shari'ar kasa da kasa.

Kotun ta ce, ana zargin Mista Putin da aikata laifukan yaki ta fuskar mayar da kananan yaran gida da kuma sauya wa wasu yaran mazauni  bayan Rasha ta mamaye yankunansu a Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.