Isa ga babban shafi

Malamar jinya ta kashe jarirai ta hanyar dirka musu guba a Birtaniya

Gwamnatin Birtaniya ta bada umurnin gudanar da bincike kan wani asibiti bayan da kotu ta samu wata malamar jinya da laifin kashe jarirai guda 7 ta hanyar dirka musu guba da kuma shirin kashe wasu karin guda 6. 

Wannan ce Lucy Letby, wadda ta kashe jarirai da gubar allura.
Wannan ce Lucy Letby, wadda ta kashe jarirai da gubar allura. via REUTERS - CHESHIRE CONSTABULARY
Talla

 

Kotun ta bayyana Lucy Letby mai shekaru 33 a matsayin fitacciyar ‘yar-ina-da kisa, wadda ta yi kaurin-suna wajen dirka wa jariran da aka sanya ta kula da su allura mai gubar sinadarin insolin ko kuma sanya musu gubar cikin madarar da suke sha. 

Iyayen jariran da Lucy ta kashe sun gabatar da sanarwar hadin-gwuiwa a kofar kotun Manchester da ke arewacin Ingila, inda suka bayyana kaduwa da matakin. 

Iyayen sun bayyana gamsuwa da hunkuncin kotun, duk da an bayyana cewar hukunta Lucy ba zai rage musu radadin kashe musu jariran da aka yi ba. 

Wani bangare na sashen kula da jarirai a asibitin da Lucy Letby ta yi aiki.
Wani bangare na sashen kula da jarirai a asibitin da Lucy Letby ta yi aiki. via REUTERS - CHESHIRE CONSTABULARY

Masu taimaka wa alkali yanke hukunci, cikin hawaye bayan kwashe kwanaki 22 suna nazari kan laifin, sun bayyana samun Lucy da aikata laifin da aka tuhume ta. 

Ana sa ran kotu ta sanar da daurin da za a mata ranar Litinin mai zuwa. 

An dai kama Lucy ce sakamakon yadda jarirai suka yi ta mutuwa a dakin asibitin da take aiki tsakanin watan Yunin shekarar 2015 zuwa Yunin shekarar 2016. 

Mai gabatar da kara ya bayyana ta a matsayin kwararriya wajen kisa, wadda ba ta barin wata shaidar da za a iya gano ta. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.