Kotu ta tuhumi Trump da yunkurin sauya sakamakon zabe
Bayan shafe shekaru biyu suna gabatar da bincike, masu gabatar da kara a Amurka sun tuhumi tsohon shugaban kasar Donald Trump da laifin yunkurin sauya sakamakon zaben shugaban kasar na jihar Georgia da ya gudana a shekarar 2020, bayan da sakamakon zaben ya nuna cewa Trump din ya sha kashi a hannun dan takarar jam’iyyar Democrats, Joe Biden.
Wallafawa ranar:
Masu gabatar da kara a Atlanta sun zargi Trump da aikata manyann laifuka 13, abin da ya kara jefa ci cikin matsaloli a gaban kuliya, kuma ya saka burinsa na neman shugabancin kasar a karo na biyu cikin hatsari.
Wasu karin mutane 118 suna fuskantar wadannan tuhume-tuhume a kan wannan bincike da ake gudanarwa, ciki har da lauyansa, Rudy Giulianni, wanda yake da hannu wajen matsa lamba a kan sakamakon zaben shekarar 2020, da kuma shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar Amurka, Mark Meadows.
Trump tare da sauran wadanda ake zargi sun ki amincewa da cewa, Trump ya fadi zabe, kuma da gangan suka rika cikin kulla munakisar sauya sakamakon zaben ta inda zai nuna cewa, shi Trump din ne ya ci zabe, kamar yadda takardar zargin ta bayyana.
Lauyoyin da aka ambaci sunayensu a kan wannan dambarwa sun ki cewa uffan, wasu daga cikinsu kuma ba a same su ba don yi wa manema labarai bayani.
Wannan batu da ya ke nema ya kai Trump ya baro dai ya samo asali ne daga zantawa ta wayar tarho da tsohon shugaban ya yi da shugaban Hukumar Zaben Jihar Georgia, Brad Raffensperger, inda yake bukatar sa ya yi aringizon kuri’u da za su goge rashin nasarar da ya yi a jihar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu