Isa ga babban shafi

An kwashe mutane da dama yayin da gobarar daji ke ci gaba da yaduwa a kan iyakar Spain da Faransa

Jami’an kashe gobara sun ce sun kwashe mutane fiye da 130, yayin da suke kokarin shawo kan gobarar daji a Portbou da ke kan iyakar Spain da Faransa.

Yadda akwa kwashe mutane a tsibirin Aegean na Rhodes da ke kudu maso gabashin Girka ranar 25 ga watan Yulin 2023.
Yadda akwa kwashe mutane a tsibirin Aegean na Rhodes da ke kudu maso gabashin Girka ranar 25 ga watan Yulin 2023. AP - Petros Giannakouris
Talla

Hukumomi daga yankin Catalonia da ke arewa maso gabashin Spain sun hada kai da takwarorinsu na Faransa yayin da gobarar ta yi barna a wani fili mai girman hekta 435.

An kwashe mutanen yankin cikin dare daga kauyuka da dama domin yin taka tsantsan sa'o'i bayan da aka ayyana gobarar zuwa kudancin Portbou, wanda tashar jirgin kasa ce da ta hada Spain da Faransa.

Iska mai karfin gaske ta taimaka wa gobarar kara ruruwa a cikin dare tare da hana jiragen da ke dauke da ruwan masu sinadarai tashi don taimakawa wajen kashe gobarar mai sarkakiya da ta shafi yankuna da dama.

A bara, mutum sama da 500 gobarar ta shafa, ta kuma yi barna a sama da hekta 300,000 a Spain, wanda ya zama tarihi mafi muni da irin wannan ibtila'i ya a Turai, bisa ga bayanan da Hukumar kashe gobara ta Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.