Isa ga babban shafi

Watsi da yarjejeniyar fitar hatsi da Rasha ta yi ganganci ne - Macron

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kwatanta ficewar Russia daga yarjejeniyar hatsi da ta kulla da Ukraine a matsayin babban ganganci. 

Shugaban Faransa Emmanuel Macron kenan.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron kenan. AP - Geert Vanden Wijngaert
Talla

Macron wanda ke jawabi bayan kammala taro tsakanin turai da kasashen Latin Amurka da Karebiya, ya ce kai tsaye Russia ta janyowa kanta bakin jini wajen kasashen da suka dogara da samun wannan hatsi, yana mai cewa Putin ya yi haka ne kawai don mayar da abinci makami.  

Bayanai na cewa tuni farashin hatsi yayi tashin farashin gwauron zabi a sassan turai saboda dakatar da wannan yarjejeniya. 

Baya ga wannan kuma shugaba Macron din ya soki yunkurin daukar hayar wata ba’amurkiya da ke da matukar kwarewa a fannin yana gizo, yayin da aka dora masa alhakin kulawa da kuma bada shawara kan yadda za’a ta alkinta bayanai da kuma habbaka bangaren kimiyya da fasahar ta. 

Macron yace yana da girmamawa matuka ga faresa Fiona Scott Morton da ke a jami’ar Yale, sai dai yana ganin akwai ‘yan asain turai da zasu iya aikin da aka dauko ta. 

Wannan dai na kara nuna irin yadda ake yiwa juna kallon hadarin kaji tsakanin turai da Amurka ta bangaren tattalin arziki da alkinta bayanai. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.