China da Amurka zasu soma tattaunawa kan dumamar yanayi a gobe litinin
Jakadan Amurka kan sauyin yanayi John Kerry ya isa birnin Beijing a yau lahadi , da nufin fara tattaunawa da kasar China kan dumamar yanayi, yayin da manyan kasashen biyu suka sake yin shawarwari mai zurfi bayan shafe watanni ana takun saka.
Wallafawa ranar:
John Kerry, wanda ke yin ziyararsa ta uku zuwa kasar China, na zuwa ne a daidai lokacin da ake ganin tasirin sauyin yanayi musamman a doron kasa, inda ake fama da zafi a sassa da dama na duniya.
Daga cikin yankunan dake fama da zafi ba a bar kasar China ba kuma babban birninta na Beijing yana fuskantar yanayin zafi kusan ma'aunin Celsius 40 tsawon makonni.
John Kerry wanda zai kasance a kasar China har zuwa ranar Laraba, zai gana da takwaransa Xie Zhenhua.
China da Amurka manyan masu gurbata muhalli na duniya, manyan kasashen duniya biyu na farko da suka kauracewa tattaunawa kan yanayin kusan shekara guda, domin a watan Agustan da ya gabata, China ta dakatar da tattaunawa kan wannan batu don nuna adawa da ziyarar da shugabar majalisar wakilan Amurka ta yi a Taiwan Nancy Pelosi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu