Isa ga babban shafi

Kona kur'ani tunzura mabiya addinin Islama ne-MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda kalaman nuna kyama da na tunzura jama’a ke ci gaba da tsananta a tsakanin al’umma, koken da ke zuwa bayan zaman da hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar ta gudanar jiya talata, game da yadda kona Qur’ani ke ci gaba da zama salon tunzura mabiya addinin Islama. 

Feuillet Coran, Maghreb ou Espagne musulmane, XIIIe ou XIVe siècle, exposé dans le cadre des « Arts de l’Islam » à Figeac.
Feuillet Coran, Maghreb ou Espagne musulmane, XIIIe ou XIVe siècle, exposé dans le cadre des « Arts de l’Islam » à Figeac. © Musée Champollion – Les Ecritures du Monde (Figeac) / Meravilles photos
Talla

Zaman Majalisar wanda Pakistan ta bukata, ya bayyana yadda Duniya ta kai kololuwa wajen ganin irin wadannan kalamai na tunzuri, inda shugaban hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar Volker Turk ke cewa matakin kona Qur’anin ba komai ya ke haddasawa ba face tunzuri da rarrabuwar kai tsakanin jama’a.  

Zaman muhawarar da hukumar ta kira na gaggawa kan wannan batu ya haddasa rarrabuwar kai a zauren Majalisar, bayan hukumar ta bukaci lallai kasashe su dauki matakin yaki da matsalar wadda ke zafafa tsamin alaka tsakanin kasashe. 

Batu na baya-bayan nan da ya ja hankalin majalisar wajen gudanar da muhawarar ta jiya shi ne yadda wani matashi dan asalin Iraqi da ke samun mafaka a Sweden ya kona Qur’anin a harabar babban masallacin kasar bisa rakiyar jami’n tsaro, a dai dai lokacin da Musulmi ke Sallar Idi ranar 28 ga watan Yunin da ya gabata.    

Pakistan wadda ta jagoranci kasashen Musulmi wajen caccakar wannan mataki tare da neman lallai a dauki matakin kawo karshen faruwar hakan, ta ce wasu tsiraru a kasashen yammaci na amfani da salon kona Qur’anin don huce haushinsu akan Musulmi ko kuma tunzura suu. 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.