Isa ga babban shafi

Mutum-mutumin da aka sanyawa fasarar AI ya ce zai iya gudanar da al’amuran duniya

Wata tawagar mutum-mutumin da aka sanyawa kirkirarriyar basirar AI da ta halarci zaman taron Majalisar Dinkin Duniya, ta ce matukar za a basu dama, babu tantama zasu iya tafiyar da al'amuran duniya ba tare da sa hannun dan adam ba.

Mutum-mutumin da aka sanyawa basirar AI ya ce zai iya gudanar da al’amuran duniya ba tare da as hannun dan Adam ba.
Mutum-mutumin da aka sanyawa basirar AI ya ce zai iya gudanar da al’amuran duniya ba tare da as hannun dan Adam ba. AP - Frank Augstein
Talla

Tawagar mutum-mutumin da suka hada da maza da mata sun ce da dan adam zai mayar da hankali wajen kirkirarsu kawai, kuma ya kaucewa yi musu katsalandan, tabbas duniya za ta inganta fiye da yadda dan adam ke tafiyar da ita.

Sai dai kuma duk da haka, sun gargadi dan adam da cewa ya kulada da kyau game da yadda ake kirkiransu cikin gaggawa, don matukar ba a yi hattara ba zasu iya za me masa illa nan gaba.

Mutum-mutumin na gada cikin mahalarta taron Majalisar Dinkin Duniya kusan kimanin dubu 3 da ke gudana a Geneva a fannin na AI, don tattauna yadda kirkirarriyar basirar AI din za ta taimaka wajen magance wasu matsaloli da duniya ke fuskata, kamar sauyin yanayi da karancin abinci da kula da zamantakewa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.