Isa ga babban shafi

Cin zarafin yara ya karu a duniya - MDD

Wani rahoton shekara-shekara na Majalisar Dikin Duniya ya bayyana cewa, an samu karuwar  take hakkin kananan yara a wasu kasashen duniya a bana.

Wasu yara 'yan Jamhuriyar Congo yayin cin abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira na wucin gadi, bayan tserewa daga muhallansu, sakamakon kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da gungun 'yan ta'adda. 10 ga Nuwamba, 2021.
Wasu yara 'yan Jamhuriyar Congo yayin cin abinci a wani sansanin 'yan gudun hijira na wucin gadi, bayan tserewa daga muhallansu, sakamakon kazamin fada tsakanin sojojin gwamnati da gungun 'yan ta'adda. 10 ga Nuwamba, 2021. REUTERS - ABUBAKER LUBOWA
Talla

A jiya Laraba ne aka yi wa Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya takaitaccen bayani game da sakamakon rahoton musamman bangaren da ke nuna yadda take hakkin yara ya tsananta a bana.

Rahotan ya bayyana cewa, a bana kadai, an ci zarafin kananan yara da aka tabbatar har sau dubu 27, adadin da shi ne mafi girma da Majalisar Dinkin Duniya ta tattara a tarihi.

Kazalika akwai kuma wani adadi na dubu 26 da ke nuna yadda kananan yara suka shiga mawuyacin hali na  bukatar daukin gaggawa.

Yanzu haka Hukumar Kula da Kananan Yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ta ce, ta shiga damuwa saboda wadannan alkaluma masu tayar da hankali.

A rahoton na bana, an samu kasashen Haiti da Nijar da sunayensu suka fito cikin jerin kasashen da suka yi kaurin-suna wajen musguna wa kananan  yaran, yayin da a bara, kasashen Habasha da Mozambique da Ukraine suka shiga cikin rahoton.

Rahoton na shekara-shekara na mayar da hankali ne kan yadda aka ci zarafin kananan yara tsakanin watan Janairu zuwa Disamba na kowacce shekara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.