Isa ga babban shafi

Shugabannin kasashen duniya 50 na halartar taron yanayi a Paris

Kimanin shugabannin kasashen duniya 50 ne tare da wakilan cibiyoyin kasa da kasa da kungiyoyin fararen hula ke halartar taron sauyin yanayi a birnin Paris na Faransa a wannan Alhamis.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron mai masaukin baki
Shugaban Faransa Emmanuel Macron mai masaukin baki © REUTERS / STEPHANIE LECOCQ
Talla

Babbar manufar mahalarta taron na bana ita ce samar da sabon tsarin tara kudade da zummar tallafa wa kasashen da suka fi fuskantar barazanar tasirin sauyin yanayi.

Ana sa ran wadannan kasashen su yi amfani da kudaden wajen yakar talauci da kuma tasirin sauyin yanayi, a daidai lokacin da kasashe masu hannu da shuni ke ci gaba da nuna aniyar mara wa takwarorinsu marasa galihu baya.

Baya ga shugabannin kasashen da wakilan gwamnati, har ila yau taron na samun halartar masana kan sauyin yanayi da ‘yan kasuwa da ma’aikatan kamfanoni masu zaman kansu.

Fadar shugaban Faransa Emmanuel Macron mai masaukin baki ta ce, wannan taron zai bayar da damar gina sabuwar kwangila tsakanin kasashen da ke kusuwar arewacin duniya da kuma wadanda ke can kudanci.

Tun a watan Nuwamban bara ne, shugaba Macron ya sanar da daukar nauyin taron jim kadan da kammala taron sauyin yanayi na COP27 wanda masana muhalli suka ce, ba su gamsu da yarjejeniyar da aka cimma a wancan taron na bara ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.