Isa ga babban shafi

Shugabannin Afrika sun mika kukansu a taron Paris

Shugabannin kasashen Nijar Benin da kuma Ghana sun mika kokensu ga taron yanayin da ke gudana a birnin Paris kan yadda manyan kasashe ke mayar da hankali wajen zuba makuden kudi a Ukraine ba tare da duba halin da nahiyar Afrika ke ciki ba, koken da ke zuwa a dai dai lokacin da Amurka ta sanar da shirin zuba karin dala biliyan 1 da miliyan 300 don farfado da tattalin arzikin kasar mai fama da yaki. 

Har yanzu shugabannin kasashen duniya na ci gaba da kokarin shawo kan matsalar sauyin yanayi.
Har yanzu shugabannin kasashen duniya na ci gaba da kokarin shawo kan matsalar sauyin yanayi. REUTERS - GONZALO FUENTES
Talla

Shugabannin kasashen na Ghana Benin da kuma jamhuriyyar Nijar yayin jawabinsu gaban taron yanayin wanda ke ci gaba da gudana a birnin Paris na Faransa sun bayyana cewa ba laifi ba ne manyan kasashen su taimakawa Ukraine amma akwai bukatar bai wa nahiyar Afrika muhimmanci lura da halin da ta ke ciki na tsananin bukatar agaji fiye da Ukraine. 

Shugabannin 3 wadanda ko a taron asusun IMF da Bankin Duniya da ya gudana cikin watan Aprilu a Washington sai da suka ja hankalin manyan kasashe game da matakin da suke dauka na fifita bukatun Ukraine akan na Afrika, sun ce akwai matukar damuwa kan  yadda kasashen ke kawar da kai ga halin da Afrikan ke ciki duk tsananin bukatar agajinta. 

Wannan kira na shugabannin Afrika 3 da suka kunshi Bazoum Mohamed na Nijar na Nana Akufo Ado na Ghana da kuma Patrice Talon na Benin, sun bayyana cewa idan har da manyan kasashe za su kwatanta makamancin tallafin da suke turawa Ukraine ga Afrika ko shakka babu da nahiyar ta fice daga wasu tarin matsaloli da suka dabaibayeta. 

Daga farkon faro yakin na Ukraine zuwa yanzu kasashen yammacin Duniya sun alkawarta sanya kudin da ya haura dala biliyan 10 don farfado da ita, dai dai lokacin da hare-haren Rasha ya kassara tattalin arzikinta da koma bayan kasha 30 a ma’aunin GDP. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.