Isa ga babban shafi

Birtaniya ta bullo da sabon tsarin kasuwanci da kananan kasashe

Birtaniya ta kaddamar da wani sabon tsarin kasuwanci mai cike da tagomashi tsakaninta da kasashe 65 matalauta domin maye tsohon tsarin da take amfani da shi a lokacin da take a matsayin mamba a Kungiyar Tarayyar Turai.

Ministan Kwadadon Kasa da Kasa na Birtaniya, Nigel Huddleston tare da  Hassan Mohammed, Ministan Kasuwanci da zuba jari na Habasha a wurin taron kaddamar da shirin a birnin Addis Ababa a ranar Litinin.
Ministan Kwadadon Kasa da Kasa na Birtaniya, Nigel Huddleston tare da Hassan Mohammed, Ministan Kasuwanci da zuba jari na Habasha a wurin taron kaddamar da shirin a birnin Addis Ababa a ranar Litinin. REUTERS - TIKSA NEGERI
Talla

Sabon tsarin kasuwancin da ake kira DCTS wanda aka kadadmar da shi a birnin Addis Ababa na kasar Habasha ya rage ko kuma janye kudaden haraji tare da sassauta dokokin cinikayya tsakanin bangarorin biyu kamar yadda wata sanarwar Ma’aikatar Kwadago ta Birtaniya ta bayyana.

A karkashin wannan shirin dai, akwai kananan kasashen duniya masu tasowa har guda 65 da ke da jumullar yawan al’umma biliyan 3 da miliyan 300 kuma akasarinsu naa yankin Afrika.

Gwamnatin Birtaniya ta ce, za ta rika samun rarar fam miliyan 770 a duk shekara saboda janye harajin kayayyakin da take shigo da su da kudinsu ya zarta fam biliyan 9, kamar suturu da abinci da kayayyakin wasa na yara.

Gwamnatin ta ce, wannan tsarin ya fi tagomashi fiye da wanda ta yi amfani da shi a can baya, lokacin da take a matsayin mamba a Kungiyar Tarayyar Turai.

A yayin kaddamar da shirin, Ministan Kwadagon Kasa da Kasa na Birtaniya, Nigel Huddleston ya ce,

za a samu guraben ayyukan yi da inganta rayuwar iyalai da fadada cinikayya a ciki da wajen Birtaniya a karkashin sabon shirin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.