Isa ga babban shafi

Kasashen Iran da Belgium sun fara musayar fursunoni

Kasashen Belgium da Iran sun fara musayar fursunoni a tsakanin su, a yau juma’a yayin da tuni mahukuntan Tehran suka saki wani ma’aikacin bada agaji dan asalin Belgium da suka kama, yayin da ita kuma Belgium ta musanya shi da wani jami’in diplomasiyyar Iran din da ke daure a kasar ta. 

Masu fafutukar kare hakkin wadanda aka tsare ba tare da kwararan hujjoji ba a kasar Amurka, yayin wata zanga-zanga.
Masu fafutukar kare hakkin wadanda aka tsare ba tare da kwararan hujjoji ba a kasar Amurka, yayin wata zanga-zanga. Getty Images via AFP - ALEX WONG
Talla

Wannan dai ta faru ne bayan da Oman ta shiga tsakannin kasashen biyu wajen ganin wannan musaya ta tabbata, karashin ma’aikatar tsaron ta. 

Tuni dai mutanen biyu suka isa kasashen su, yayin da ake shirin sada su da iyalan su nan ba da jimawa ba. 

Masarautar Oman ta yaba da wannan sauyin, tana mai cewa irin wannan ake bukatar gani a duniya don tabbatar da tsaro da kuma samun jituwa tsakanin kasashe. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.