Yadda mabiya addinin kirista suka gudanar da bikin Easter
A kowacce shekara, mabiya addinin kirista kan gudanar da bukuwa da kuma hutu a watan Afrilu da sunan bukukun Good Friday da kuma Easter, duk domin tunawa da Yesu Almasihu.
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:03
Abin da littafin tsohon alkawari ya ce, ana fara gudanar da wannan biki ne a rana ta uku da bizne shi, bayan da Romawa suka gicciye shi a wani waje da ake kira Calvary ko kuma Golgotha da ke wajen birnin Kudus.
Mabiya addinin kirista a fadin duniya dai na fara gudanar wannan biki ne tun daga ranar Alhamis, inda suke kammala shi ranar litinin, wanda ssuke kira Easter Monday kenan.
Wakilin RFI Bilyaminu Yusuf ya duba muhimmancin wannan rana, inda ya hada rahoto a kai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu