Isa ga babban shafi

Kotu a Rasha ta samu dan jaridar Amurka da laifin leken asiri

Kamfanin dillancin labaran Rasha ya bayar da rahoton cewa, Moscow ta tuhumi dan jaridar Amurka Evan Gershkovich da laifin leken asiri a hukumance, duk da cewa ya musanta zargin da ake masa.

Evan Gershkovich, dan jaridar Amurka da ke tsare a kasar Rasha.
Evan Gershkovich, dan jaridar Amurka da ke tsare a kasar Rasha. AFP - DIMITAR DILKOFF
Talla

Kamen da aka yi wa wakilin Wall Street Journal Evan Gershkovich ya jawo cece-ku-ce daga kafafen yada labarai da kungiyoyin kare hakki dan adam, da kuma jami'an gwamnati a Washington.

"Masu bincike na FSB sun tuhumi Gershkovich da laifin leken asiri don amfanin kasarsa," in ji kafar yada labarai ta kasar Rasha TASS.

"Ya musanta dukkan zarge-zargen da ake masa, kuma ya bayyana cewa yana gudanar da ayyukan jarida a Rasha ne kawai," in ji TASS.

Ana dai kallon kamen Gershkovich a matsayin wani gagarumin ci gaba na murkushe kafafen yada labarai a kasar ta Rasha.

Cafke dan jaridar dai na zuwa ne yayin da alakar Rasha da Amurka ta yi tsami sosai saboda yakin da ake yi a kasar Ukraine.

Washington ta dade tana zargin Moscow da kame Amurkawa ba bisa ka'ida ba domin amfani da wannan damar wajen musayar 'yan Rashan da ake tsare da su a Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya yi kira da a saki Gershkovich a ranar Juma'a, yayin da fadar White House ta bayyana zargin da ake masa a matsayin abin dariya.

Sai dai gwamnatin Rasha ta ce ba bu wata ma'ana a kokarin da wasu kasashe ke yi na tursasa Moscow ta sako dan jaridar, bayan da ta same shi da laifin leke asiri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.