Guterres ya caccaki manyan kasashe kan ci da gumin kanana
Magatakardan Majalisar Donkin Duniya Antonio Guterres ya caccaki kasashe masu hannu da shuni da arzikin makamashi a game da yadda suke ci da gumin takwarorinsu matalauta ta wajen tsawwala musu kudin ruwa tare da ruguza farashin mai.
Wallafawa ranar:
Da yake jawabi a Doha, babban birnin Qatar, Speaking Guterres ya shaida wa jagororin kasashe marasa galihu sama da 40 cewa, kamata ya yi kasashe masu karfin arziki su sama musu dala biliyan dubu 5 duk shekara don taimaka wa wadanda suka tauye a bangaren bunkasar tattalin arziki da samara da mahimman ayyuka.
An saba gudanar da taron koli na kasashen da suka fi koma baya a fannin ci gaba bayan duk shekaru 10, amma aka daga har sau, tun a shekarar 2021 saboda annobar Coronavirus.
Afghanistan da Myanmar, 2 daga ckin kasashe marasa karfin tattalin arziki da ba su halarci wannan taro na Doha ba, saboda rashin amincewa da gwamnatocinsu a majalisar dinkin duniya.
Babu wani shugaba na daya daga cikin manyan kasashe masu karfin tattalin arziki da ya halarci wannan taro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu