Isa ga babban shafi

Guterres ya bude taron Majalisar Dinkin Duniya da batun yaki

Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 da shugabannin kasashen suka halarta ya mayar da hankali kan yake-yaken da ke wakana a Turai tun bayan yakin duniya na biyu, wato batun yakin Rasha a Ukraine.

Babban sakataren MDD Antonio Gutteres kenan
Babban sakataren MDD Antonio Gutteres kenan REUTERS - POOL
Talla

Yakin ya haifar da matsalar karancin abinci a duniya tare da cece-kuce tsakanin manyan kasashen duniya, abin da ba a saba gani ba tun bayan yakin cacar baka.

A jawabin da ya yi gabanin taron, Guterres ya ce duniya na cikin “babban hadari,” kuma dole ne a magance tashe-tashen hankula da bala’o’in yanayi, da karuwar talauci da rashin daidaito, tare da magance rarrabuwar kawuna tsakanin manyan kasashe, abinda ke kara ta’azzara tun bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

Daga cikin wadanda za su gabatar da jawabi a rana ta farko na taron, akwai shugaban Faransa, Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz, wato shugabannin kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki na Tarayyar Turai, wadanda suka yi yunkurin kakaba takunkumi mai tsauri kan mamayar da Rasha ta yi a Ukraine.

Masu gabatar da jawabai na ranar Talatar akwai shugaban kasar Brazil Jair Bolsanaro, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.