Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kamfanoni su daina rufa-rufa a kan dumamar yanayi

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a kawo karshen rufa-rufar da kamfanoni ke yi kan gurbatacciyar iskar da suke fitarwa, wadda ke tsananta matsalar dumamar yanayi.

Antonio Guterres, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya.
Antonio Guterres, babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya. AP - Thomas Hartwell
Talla

Kiran na Antonio Guterres ya zo ne jim kadan bayan da wani rahoton kwararru ya bayyana cewar kamfanoni ba za su iya cimma muradin rage dumamar yanayi zuwa matakin sifili ba, muddin suka cigaba da aiwatar da matakan da suka hada da zuba jari kan amfani da nau’ikan makamashin da suke gurbata yanayi, sare bishiyoyi, da kuma cigaba da bulbular da iska mai guba, a maimakon rage matsalar.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniyar ya ce kamata ya yi masana’antu da mahukuntan birane da yankuna su sabunta alkawuran da suka dauka na tabbatar da cewa sun dakile gurbata yanayi zuwa matakin sifili a cikin shekara guda.

Kwamitin kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya kafa bayan taron sauyin yanayi na duniya da ya gudana a birnin Glasgow a shekarar bara, ya bayyana aniyar shatawa kamfanonin da sauran hukumomi na kasa da kasa jan layi dangane da kiyaye aikata abubuwan da suke rura wutar matsalar sauyin yanayi.

A bayan bayan nan, masu faftukar yaki da matsalar canjin yanayi na kungiyar Net Zero Tracker, suka ce karuwar alkawuran da ake yi a cikin 'yan watannin nan yana nufin kusan kashi 90 na kasashen duniya  na dauke da alkawarin rage fitar da iskar Carbon mai guba, matsayar da aka cimma tun a lokacin babban taron duniya kan matsalar sauyin yanayi cikin shekarar 2015 a birnin Paris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.