MDD ta karrama mutane dubu 2 da 300 da suka mutu a girgizar kasa
Majalisar Dinkin Duniya ta yi shiru na tsawon minti guda domin karrama sama da mutane dubu 2 da 300 da suka rasa rayukansu sakamakon ibtila’in girgizar kasa da ya auku a kasashen Syria da Turkiya a wannan Litinin.
Wallafawa ranar:
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya ce, yanzu haka, tawagarsu na can na bada agaji, yana mai kira ga kasashen duniya da su tallafa wa dubban iyalan mutanen da gagarumin ibtila’in ya rutsa da su.
Kawo yanzu an tattara alkaluman sama da mutane dubu 2 da 300 da suka mutu a kasashen Syria da Turkiya sakamakon girgizar kasar wadda ta auku da asubahin yau, yayin da aka bayyana ta a matsayin mafi muni da aka gani cikin shekaru 100 a wannan yanki.
A kasar Turkiya kadai, hukumomi sun tabbatar da asarar rayukan mutane dubu 1 da 498 , inda kuma a Syria mamatan suka kai 810.
Akwai dai yiwuwar adadin mamatan ya karu, ganin cewa, ana ci gaba da aikin zakulo mutanen da suka makale karkashin buraguzan gine-ginen da suka rushe sakamakon girgizar kasar mai karfin maki 7.8.
Da dama daga cikin mutanen gari sun shiga aikin ceto wadande ke da sauran numfashi, kuma aikin ceton ya fi wahala a Syria saboda karancin kayayyakin aiki a cewar rahotanni.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu