Mutane akalla uku ne suka mutu sakamakon ruwan sama a New Zealand
Ruwan sama kamar da bakin kwarya da ba a taba ganin irinsa ba sun yi sanadin mutuwar mutane akalla uku, yayin da ake ci gaba da neman wasu yanzu haka a Auckland, birni mafi yawan jama'a a New Zealand, sanarwa daga ji Firayim Minista Chris Hipkins a yau asabar.
Wallafawa ranar:
'Yan sanda sun ce an gano gawarwaki biyu a yankunan arewacin kasar sannan na uku da ya mutu ya mutu sakamakon zaftarewar kasa kusa da tsakiyar Auckland.
Filin jirgin saman yankin, mafi girma a kasar, an sake bude wani bangare bayan rufe shi na wani lokaci a yau asabar.
Saboda dalilai na tsaro, an soke wasannin kade-kade da fitaccen mawakin Birtaniya Elton John, wanda aka shirya a filin wasa na Auckland a ranakun Juma'a da Asabar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu