Isa ga babban shafi

Murabus din Firaministar New Zealand ya girgiza 'yan kasar

Al'ummar New Zealand sun girgiza bayan Firaministar kasar Jacinda Ardern ta sanar da aniyarta ta yin murabus daga kujerarta a daidai lokacin da al'ummar ke matukar kaunar ta.

Firaministar New Zealand, Jacinda Ardern.
Firaministar New Zealand, Jacinda Ardern. REUTERS - LOREN ELLIOTT
Talla

A wani taro da ta yi da mambobin jam'iyyarta ta Labour, Ardern mai shekaru 42 ta bayyana cewa, lada ta isa haka domin kuwa tana son ta je ta huta.

Ana jinjina mata kan irin namijin kokarin da ta yi wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar musamman lokacin da wani dan ta'adda ya kaddamar da farmaki kan Musulmai a Masallaci tare da kashe kimanin 50 daga cikinsu.

Kazalika ta taka rawar gani wajen yaki da annobar Covid-19 da kuma tunkarar wasu bala'o'i masu aukuwa da kansu a kasar.

Firaministar ta ce, tana sa ran yin ban-kwana da kujerarta kafin ranar 7  ga watan Fabairu mai zuwa, matakin da ke zuwa kasa da shekaru uku da ta lashe zaben kasar da gagarumin rinjaye a wa'adi na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.