Mawakin Amurka ya fusata 'yan Ghana a fadar shugaban kasarsu
Mafi yawan al’ummar Ghana sun fusata, bayan da wani shahrarren mawakin Amurka mai suna Meek Mill ya yada wani gajeren faifan biyo yana rera waka a ciki da harabar ginin fadar shugaban kasar ta Ghana da ke birnin Accra.
Wallafawa ranar:
Hoton bidiyon ya nuna mawakin da tawagarsa tsaye a bayan minbarin da shugaban kasar Ghana ke hawa domin gabatar da jawabi, da kuma babban dakin taro na fadar shugaban kasa.
Tuni ‘yan Ghana suka yi ta caccakar mawakin da shugaban kasarsu a shafukan sada zumunta, yayin da wasu bayanai ke cewa, tuni ya janye faifain bidiyon daga shafinsa na Instagram.
A karshen watan Disamban da ya gabata, wannan mawaki ya gabatar da wasa a birnin Accra, kuma ana kyautata zaton a lokacin ne ya nadi hotunan bidiyon a fadar shugaban kasar.
A jiya Lahadi ne mawakin ya wallafa wani sashi na faifain bidiyon a shafinsa na Instagram, yana mai cewa, nan kusa zai saki cikakkiyar sabuwar wakar ga duniya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu