Isa ga babban shafi

Kotu a Faransa na tuhumar wanda ake zargi da kisan Kurdawa a birnin Paris

Faransa ta tuhumi wani da ake zargin dan bindiga ne a ranar Litinin da ta gabata da kisan wasu Kurdawa uku a birnin Paris a makon da ya gabata, daidai lokacin da daruruwan mutane suka yi maci a babban birnin kasar Faransa domin nuna girmamawa ga wadanda abin ya shafa.

Masu fafutuka na Kurdawa rike da tutoci da kayan kade-kade don karrama wasu mata uku da aka harbe a shekarar 2013.
Masu fafutuka na Kurdawa rike da tutoci da kayan kade-kade don karrama wasu mata uku da aka harbe a shekarar 2013. AP - Lewis Joly
Talla

Mutumin mai shekaru 69 ya amsa kiyayyar da yake yi wa ‘yan kasashen waje, abin da ya sa ya shafe kusan yini guda a wani asibitin mahaukata kafin a mayar da shi hannun ‘yan sanda, in ji hukumomi.

Majiyar shari’a ta ce alkali ya tuhumi mutumin da laifin kisan kai, yunkurin kisan kai saboda kabilanci, da kuma sayen makamai ba tare da izini ba.

Harbin da aka yi a wata cibiyar al'adu ta Kurdawa da wurin gyaran gashi a ranar Juma'a ya haifar da firgici a gunduma ta 10 mai cike da shaguna da gidajen cin abinci da kuma dimbin al'ummar Kurdawa.

Wasu mutum uku sun jikkata a harin amma babu wanda ke cikin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai, yayin da aka sallami mutum guda daga cikin su yanzu haka.

Rikicin dai ya sake farfado da bala'in kisan gillar da aka yi wa Kurdawa guda uku a shekara ta 2013 wanda da yawa ke dora alhakinsa kan Turkiyya.

Kazalika al’ummar kasar sun nuna bacin ransu ga jami’an tsaron Faransa, inda suka ce ba su yi wani abu da ya wuce kima ba wajen hana harbin.

A ranar Asabar masu zanga-zangar da suka fusata sun yi arangama da 'yan sanda a tsakiyar birnin Paris bayan wani taron karramawa.

A ranar litinin daruruwan mutane ne suka yi maci a gundumar ta 10, suna rera taken "Shahidanmu ba sa mutuwa a banza" da harshen Kurdawa tare da neman gaskiya da adalci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.