Isa ga babban shafi

China da Rasha sun fara atisayen Sojin ruwa don martani ga Amurka

Babban hafsan sojin Rasha Valery Gerasimov ya ce kasar na gudanar  da atisayen hadin gwiwar jiragen ruwan yakin tsakanin ta da China, da nufin mayar da martani ga yadda sojojin Amurka ke kara kutsawa yankin Asiya da tekun Pasific.

Atisayen hadaka tsakanin sojin ruwan Rasha da na China.
Atisayen hadaka tsakanin sojin ruwan Rasha da na China. REUTERS/Stringer
Talla

Rasha ta sanar da aikewa da jiragen yaki na ruwa da dama domin shiga atisayin da aka faro daga ranar 21 ake kuma sa ran zai kai har zuwa 27 ga watan Disamba a gabar tekun kasar China, domin karfafa hadin gwiwar sojojin ruwan su.

Ma'aikatar tsaron kasar ta ce atisayen da za su gudanar ya hada da harba manyar makamai masu linzami da manyan bindigogi da kuma yadda za’a dakile hare-haren jiragen ruwa.

Kasashen China da Rasha sun kara dankwan zumuntar da ke tsakanin su ne a shekarun baya-bayan nan, a wani bangare na abin da suka kira dangantakar da ba ta da iyaka, wadda ke zama mai cin karo da karfin ikon Amurka a duniya.

A farkon makon nan ne tsohon shugaban Rasha Dmitry Medvedev ya kai ziyara kasar China domin ganawa da shugaba Xi Jinping don tattaunawa wacce Medvedev ya ce ta hada da batun tsaron kasa da kasa da kuma rikicin Ukraine.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.