Isa ga babban shafi

A shirye na ke na sauka daga jagorancin Twitter idan na samu magaji- Musk

Attajirin Amurka mamallakin kamfanin Twitter Elon Musk ya bayyana cewa a shirye ya ke ya sauka daga jagorancin kamfanin matukar ya samu wanda zai maye gurbinsa, matakin da ke zuwa bayan kada kuri’ar da ta nuna bukatar saukarsa daga jagorancin kamfanin.

Shugaban kamfanin Twitter Elon Musk.
Shugaban kamfanin Twitter Elon Musk. © Miguel Roberts / The Brownsville Herald, via AP
Talla

A ranar 27 ga watan Oktoban da ya gabata ne Musk ya karbi ragamar jagorancin kamfanin na Twitter bayan sayensa kan dala biliyan 44, said ai sabbin matakan da ya dauka sun haddasa masa yamutsi musamman matakinsa da korar rabin ma’aikatan kamfanin da kuma dawo da asusun wasu masu tsattsauran ra’ayi da kamfanin ya dakatar da su a baya.

Haka zalika matakin Musk na dakatar da ‘yan jaridun dandalin da ke sukarsa a dandalin da kuma bukatar sa ta neman sanya kudi kan abubuwan da a baya akeyi kyauta a twitter, suma sun haddasawa sabon jagoran matsala.

A wani sako da ya wallafa, Elon Musk ya ce a shirye ya ke ya sauka daga jagorancin Twitter idan har zan samu wani da zai yi karancin azanci wajen karbar ragamar kamfanin, yana mai cewa zai ci gaba da jan ragamar sashen da ke kula da rumbunan bayanai da kuma manhajojin kamfanin na Twitter.  

Sakamakon kada kuri’ar da masu amfani da manhajar ta Twitter suka gudanar ya nuna cewa kashi 57 na masu asusun kamfanin sun zabi saukar Musk daga shugabanci kasa da watanni 2 bayan sayen kamfanin kan dala biliyan 44.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.