Isa ga babban shafi

Masu amfani da Twitter sun kada kuri'ar sauke Elon Musk daga shugabanci

Masu amfani da dandalin sadarwar Twitter sun kada kuri’ar neman kawar da mamallakin manhajar Elon Musk daga shugabancin kamfanin, makwanni kalilan bayan attajirin Amurkan ya karbi ragamar kamfanin.

Elon Musk shugaban kamfanin sada zumunta na Twitter.
Elon Musk shugaban kamfanin sada zumunta na Twitter. AFP - OLIVIER DOULIERY
Talla

Kada kuri’ar wanda Musk ya tsara da kansa ya kuma sha alwashin mutunta dukkanin sakamakon da zaben ya bayar, alkaluma sun nuna cewa kashi 57.5 na masu amfani da manhajar wanda ke wakiltar asusun jama’a miliyan 17 sun zabi saukarsa daga shugabancin kamfanin.

Musk wanda ke jagorancin kamfanin kera motoci na Tesla da kuma kamfanin sarrafa rocket na SpaceX har zuwa yanzu bai fito fili ya ce komi game da sakamakon kada kuri’ar ba.

A wani sako da Musk haifaffen Afrika ta kudu ya wallafa a shafinsa na gabanin kada kuri’ar ta jiya litinin, ya bayyana cewa tambayar ba ita ce nemarwa Twitter jagora ba, tambayar ita ce nemarwa kamfanin jagoran da zai iya tafiyar da shi yadda ya dace.

Tun a ranar 27 ga watan Oktoba ne Elon Musk yak arbi ragamar jagorancin kamfanin bayan kammala sayensa sai dai takaddama ta dabaibaye jagorancinsa musamman bayan korar fiye da rabi na ma’aikatan kamfanin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.