Isa ga babban shafi

Musk ya ce zai maido da shafukan twitter da aka dakatar

Sabon mai shafin Twitter Elon Musk ya sanar da yammacin jiya Juma'a cewa zai maido da asusun ajiyar 'yan jarida da dama da aka dakatar a wannan dandalin sada zumunta na Twitter, bayan ya zarge su da jefa iyalansa cikin hadari.

Ellon Musk Shugaban Twitter
Ellon Musk Shugaban Twitter REUTERS/Monica Almeida
Talla

Elon Musk ya kaddamar da kada kuri'a a shafin Twitter don tambayar ko zai dawo da asusun da aka dakatar nan da nan ko kuma cikin mako guda. Kusan kashi 59 cikin 100 na masu amfani da Intanet miliyan 3.69 da suka shiga binciken sun amsa cewa ya kamata ya mayar da su cikin gaggawa.

Da alama an sake dawo da wasu asusun, kamar na tsohon ɗan jaridar Vox Aaron Rupar.

An dakatar da wasu 'yan jaridar Amurka goma sha biyu daga shafukan sada zumunta. Daga cikinsu akwai ma'aikatan yada labarai kamar CNN Donie O'Sullivan, New York Times Ryan Mac, Washington Post Drew Harwell da 'yan jarida masu zaman kansu.

Rikicin ya fara ne ranar Laraba lokacin da Elon Musk ya sanar da cewa ya dakatar da @elonjet, asusun da ke ba da rahoto kai tsaye kan tafiye-tafiyen jirginsa na sirri.

Elon Musk ya ba da hujjar dakatar da asusun ta hanyar da'awar cewa suna jefa lafiyarsa da na danginsa cikin hatsari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.