Isa ga babban shafi

Dan shugaban Uganda ya bijirewa haramcin amfani da Twitter bayan haddasa tarzoma

Janar Muhoozi Kainerugaba na kasar Uganda, da ga shugaban kasar, ya ce babu wanda zai hana shi yin gaban kansa wajen aikata abinda ya ke ganin ya dace, walau a shafukan sada zumunta ko a zahiri, kalaman da ke matsayin kalubalantar haramcin da mahaifinsa ya yi masa na tsoma baki a harkokin da basu shafe shi ba.

Janar Muhoozi Kainerugaba dan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.
Janar Muhoozi Kainerugaba dan shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni. © Hajarah Nalwadda / AP
Talla

Kalaman na Janar Muhoozi na zuwa ne kwana guda bayan da mahaifinsa, shugaba Yoweri Museveni, ya ba da umarnin haramta mishi yin tsokaci kan harkokin gwamnati a shafinsa na Twitter.

Matakin na Museveni ya biyo bayan yadda Janar Kainerugaba ya yi amfani da shafinsa na Twitter wajen yin barazanar mamaye kasar Kenya da ke makwabtaka da Kampala lamarin da ya yamutsa hazo tare da sanya shakku a zukatan jama'a.

Tuni kalaman na Janar Kainerugaba ya tilastawa gwamnatin Uganda neman afuwar jama'a da kuma taron diflomasiyya don kawar da duk wani shakku kan batun.

Janar Kainerugaba dai ya yi kaurin suna a shafinsa na twitter wajen tsoma baki ko kuma yin tsokaci kan lamurran da ke janyo cece-kuce a ciki da wajen kasar ciki har da nuna goyon baya ga mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, da kuma 'yan tawayen Tigray da ke yaki da gwamnatin Habasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.