Isa ga babban shafi

Kamfanin Twitter ya dawo da shafin Donald Trump

Kamfanin Twitter ya dawo da shafin Donald Trump a ranar Asabar bayan da sabon shugaban kamfanin, Elon Musk ya gudanar da zaben raba gardama inda mafi yawan masu kada kuri'a suka goyi bayan matakin, kwanaki bayan da tsohon shugaban na Amurka ya sanar da wani yunkurin sake tsayawa takarar shugabancin kasar.

Tsohon shugaban Amurka kenan, Donald Trump
Tsohon shugaban Amurka kenan, Donald Trump AP - Seth Wenig
Talla

An dakatar da Trump daga dandalin ne a farkon shekarar da ta gabata saboda rawar da ya taka a harin da wasu gungun magoya bayansa suka kai majalisar dokokin kasar Amurka a ranar 6 ga watan Janairun da ya gabata.

"Mutane sun bayar da goyon baya. Za a mayar da shafin Trump kan aiki," a cewar Musk da ya wallafa a shafinsa na Twitter jim kadan bayan kammala zaben na sa'o'i 24.

"Vox Populi, Vox Dei," yana maimaita wani karin maganar Latin da ya wallafa ranar Juma'a ma'ana "Allah ya amsa rokon mutane."

Fiye da mutane miliyan 15, daga cikin miliyan 237 masu amfani da Twitter a kullum ne, suka kada kuri'a kan ko za a maido da shafin tsohon shugaban na Amurka da ke janyo cece-kuce, inda kashi 51.8 suka amince da hakan yayin da kashi 48.2 cikin 100 suka nuna adawa.

Trump, wanda ke da mabiya fiye da miliyan 88, a lokacin da aka dakatar da shafin nasa, ya yi amfani da Twitter a matsayin mai magana da yawunsa a lokacin da yake shugaban kasa, inda yake yada manufofinsa, kai hari ga abokan hamayyar siyasa da kuma aika sako ga dimbin magoya bayansa.

Kuri'ar jin ra'ayin jama'a ta Musk ta nemi a ba da amsa mai sauki na "e" ko "a'a" ga sanarwar "Mayar da tsohon shugaban na Amurka wato Donald Trump," wanda shugaban kamfanin kuma hamshakin attajirin na Twitter ya wallafa a ranar Juma'a.

- Ina da nawa shafin sada zumunta'

Sai dai Mista Trump ya ce ba zai koma dandalin da ya shahara ba amma a maimakon haka ya ci gaba da zama a kafar sadarwarsa ta Truth Social, wacce aka kaddamar bayan an dakatar da shi daga Twitter.

Da yake jawabi a wani faifan bidiyo a wurin taron hadin gwiwa na Republican da aka gudanar a Las Vegas, Trump ya ce ya yi maraba da zaben kuma dama shi yana kaunar sabon shugaban kamfanin na Twitter wato Ellon Musk, amma da alama ba zai komawa shafin nasa ba.

Dangane da ko zai koma dandalin sai ya ce: "Ban gan shi ba saboda ban ga dalilin yin hakan ba."

Trump dai bai wallafa komai a shafinsa na Twitter ba da yammacin jiya Asabar, ko da yake ya bayyana wasu sakonnin da ba su da alaka da su a shafinsa na True Social, da suka hada da labaran ra'ayi da ke sukar nadin da ma'aikatar shari'a ta Amurka ta yi na ba da shawara na musamman a cikin wannan makon domin binciken rawar da ya taka a harin na Capitol.

Amma da yawa daga cikin abokan siyasarsa suna nuna alamar dawowar sa fagen fama.

Musk ya dawo da wasu shafukan da aka dakatar, ciki har da na mai wasan barkwanci Kathy Griffin.

- Twitter na cikin hatgitsi –

Musk, wanda kuma shi ne Shugaban Kamfanin Tesla da SpaceX, ya sha suka kan sauye-sauyen da ya gudanar a kamfanin na Twitter dake California, wanda ya saya kasa da wata guda da ya wuce kan dala biliyan 44.

Tun daga wannan lokacin, ya kori rabin ma'aikatan Twitter 7,500 tare da yin watsi da tsarin aiki daga gida, yayin da yunkurinsa na sake fasalin kamfanin ya fuskanci koma baya da kuma jinkiri.

Daruruwan ma'aikata ne suka yi murabus maimakon yarda da bukatun Musk na yin aiki na tsawon kwanaki ba tare da hutawa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.