Isa ga babban shafi

ICC ta yi gargadi a kan samar da kotu na dabam a kan rikin Ukraine da Rasha

Mai shigar da kara na kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC Karim Khan, ya ce yunkurin samar da wata kotu ta musamman da za ta gudanar da bincike gameda rikicin Ukraine akan Rasha bai da ce ba.

Masu gabataar da kara na kotun ICC a yayin taronsu a birnin Hague.
Masu gabataar da kara na kotun ICC a yayin taronsu a birnin Hague. REUTERS - EVA PLEVIER
Talla

Shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen a makon da ya gabata ta gabatar da shawarar samar da kotu ta musamman da majalisar dinkin duniya za ta marawa baya don tuhumar shugabannin Rasha bisa aikata laifukan yaki gameda mamayar da ta yi wa Ukraine.

Sai dai mai shigar da kara na kotun ta ICC Khan, ya bukaci kasashen duniya da su kauracewa wancan yunkuri da kuma bayar da kudade domin kotun ta ICC tana gudanar da binciken laifukan yaki da cin zarafin bil adama a Ukraine.

Kungiyar EU ta ce shugabanni irin su shugaban Rasha Vladimir Putin za su iya samun kariya daga tuhumar da ake musu a gaban kotun ICC.

Khan ya ce kungiyar EU bata fahimci abinda dokar kariya ke Magana ba a kai, don haka shi da kansa zayyiwa von der Leyen karin haske.

Ukraine da wasu kasashen yammacin duniya sun goyi bayan kiraye-kirayen  kafa kotun ta musamman kuma Netherlands ta yi tayin bata matsugunni.

Sai dai tuni Moscow ta ce shirye-shiryen samar da kotun ya sabawa doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.