Isa ga babban shafi

Tsohon shugaban China Jiang ya mutu yana da shekaru 96

Tsohon shugaban China Jiang Zemin ya mutu a wannan Larabar yana da shekaru 96 kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka rawaito, inda suka bayyana shi a matsayin fitaccen dan kwamunisanci wanda ya taimaka wajen kawo karshen zanga-zangar neman tabbatar da demokuradiya a shekara ta 1989.

Jiang Zemin.
Jiang Zemin. REUTERS - STRINGER
Talla

Jiang ya dare kan karagar mulkin China ne bayan kawo karshen murkushewar da aka yi wa masu zanga-zanga a dandalin Tiananmen, lokacin da sojoji suka yi amfani da karfin da ya wuce kima kan jama’a.

Jam’iyyar Kwamunisanci da ke mulkin kasar, ita ce ta sanar da mutuwar Jiang sakamakon fama da cutar kansar jini, yayin da likitoci suka gaza ceto sa daga larurarsa.

Sanarwar da jam’liyyar ta fitar ta kwarara yabo ga marigayin da ta bayyana a matsayin jajirtaccen shugaba, mabiyin akidar Kar Marx, kuma kwararren ta fannin shirya aikin soji, sannan masanin diflomasiya wanda ya sha gwagwarmayar yakin tabbatar da kwamusanci.

Mutuwarsa dai na zuwa ne a daidai lokacin da China ke fuskantar ta’azzarar zanga-zangar nuna adawa da kullen Korona wadda ta rikide zuwa kiraye-kirayen bai wa jama’ar kasar  cikakken ‘yancinsu na siyasa.

Wannan zanga-zangar ita ce mafi girma da aka gani a China tun wadda aka yi a shekarar 1989, ,lokacin da ‘yan kasar suka nemi a tabbatar da tsarin demokuradiya a kasar.

Marigayin ya jagoranci China wajen ganin ta shiga sahun manyan kasashen duniya masu karfin tattalin arziki, amma dai har yanzu wasu na ci gaba da sukar lamirinsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.