Isa ga babban shafi

MDD ta gargadi China kan murkushe masu zanga-zanga

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci China da ta kauce wa garkame mutanen da ke gudanar da zanga-zangar lumana a kasar, inda suke neman ‘yancinsu na siyasa da kuma kawo karshen dokar kullen annobar Korona da suka ce ta yi musu tsauri.

Wasu daga cikin masu gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin China.
Wasu daga cikin masu gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnatin China. REUTERS - THOMAS PETER
Talla

Kiran na Majalisar Dinkin Duniya na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Beijing ke kokarin shawo kan zanga-zangar wadda ta karade sassan kasar ta China.

Jama’a sun shiga zanga-zangar a manyan biranen kasar, inda suka yi dafifi a kan tituna da harabar makarantun jami’o’i, a wani al’amari da ba a taba ganin irinsa ba tun shekarar 1989, lokacin da aka murkushe mutanen da suka yi zanga-zangar neman tabbatar da demokuradiya a kasar.

A jiya Lahadi, an ga yadda masu boren suka yi arangama da jami’an ‘yan sanda.

Yanzu haka Ofishin Kare Hakkin Bil’ama na Majalisar Dinkin Duniya na cewa, kar a kuskura a garmake wani saboda zalunci bayan ya fito karara yana neman hakkinsa.

Ofishin ya bai wa gwamnatin China shawara cewa, ta shirya muhawara a sassan kasar musamman tare da matasa kafin daukar matakan da suka shafi al’umma.

A makon jiya, an samu wata gobara da ta lakume rayukan jama’a a Urumqi, babban birnin Xinjiang da ke yankin arewa maso yammacin Chinaa, lamarin da ya fuskata jama’a da ke ganin cewa, dokar kulle ce ta hana a kai dauki domin ceto mutanen da suka mutu a ibtila’in.

Daga cikin kasashen da suka mayar ta martani har da Amurka wadda ta ce, mutanen China na da ‘yancin yin zanga-zanga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.