Isa ga babban shafi

Masu zanga-zangar adawa da dokokin Corona sun mamaye kasar China

Daruruwan mutane ne suka fito kan tituna a biranen Beijing da Shanghai a ranar Lahadi don nuna rashin amincewarsu da manufar hukumomin kasar China na kulle saboda da cutar COVID-19.

Wasu daga cikin masu zanga-zabga a China
Wasu daga cikin masu zanga-zabga a China Eva Rammeloo via REUTERS - EVA RAMMELOO
Talla

Daruruwan mutane sun yi zanga-zanga a babbar jami’ar Tsinghua ta birnin Beijing don nuna rashin amincewarsu da kulle a yau Lahadi, da misalin karfe 11:30 na safe ne dalibai suka fara nuna damuwa yayin wannan ganggami.

Mahalarta taron sun rera taken kasa,suka kuma rera wakar "'yanci zai yi nasara, muna son 'yanci", in ji su.

A birnin Shanghai da yammacin ranar Lahadi, daruruwan mutane ne suka taru don gudanar da wani abin da ake ganin tamkar zanga-zangar ce ta yi shiru, kamar yadda wani ganau ya shaida wa AFP, kusa da inda aka yi zanga-zangar sa'o'i kadan da suka wuce.

Masu zanga-zangar rike da takarda da fararen furanni sun tsaya shiru a wurare da dama, in ji mutumin bisa sharadin sakaya sunansa, kafin daga bisani jami’an ‘yan sanda su tashi don share hanyoyin da aka toshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.