Isa ga babban shafi

MDD na shirin yi wa Iran binciken kwa-kwaf

Majalisar Dinkin Duniya ta ce, hukumomin Iran sun garkame kimanin mutane dubu 14 da suka shiga zanga-zangar nuna bacin rai kan mutuwar Mahsa Amini,  wadda ta gamu da ajalinta a hannun jami’an tsaron kasar bayan sun kama ta saboda rashin sanya kallabi.

Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk.
Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil'adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk. AP - Marwan Ali
Talla

A wani taron gaggawa da ya gudana a yau Alhamis, Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Turk ya bukaci kawo karshen cin zarafin masu zanga-zangar  a Iran.

Hukumar Kare Hakkin Bil’adamar ta shirya taron ne domin nazari  kan yiwuwar kaddamar da gagarumin binciken kasa da kasa kan Iran bisa zargin ta da  kashe masu zanga-zanga.

Mista Turk ya ce, dole ne a kawo karshen amfani da karfin da ya wuce kima kan al’ummar Iran.

Mista Turk ya kara da cewa, Iraniyawa na neman sauyi ne, abin da ya sa suke nuna jarumta, a don haka ya kamata gwamnatin kasar ta saurare su a cewarsa.

Jami’an tsaron Iran sun yi amfani da harsashen gaske da borkonon tsohuwa wajen tarwartsa masu zanga-zangar kamar yadda Hukumar Kare Hakkin Bil’adamar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce.

Hukumar ta ce, wasu majiyoyinta masu tushe sun bada alkaluman mutane sama da 300 da suka rasa rayukansu da suka hada da kananan yara 40 a dalilin boren da suka yi kan mutuwar Amini, abin da hukumar ta ce, sam ba za ta lamunta ba.

Yanzu haka sama da mutane dubu 14 na nan garkame a hannun hukumomin Iran bayan an kama su a cikin masu zanga-zangar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.