Isa ga babban shafi

Kasashen Turai za su samar da shu'umin tauraron dan adam

Faransa, Jamus da kuma Italiya sun sanar da wani gagarumin shirin samar da tauraron dan adam na zamani da zai rika yin gogayya da na sauran kasashen duniya wajen gudanar da ayyuakn bincike a sararin samaniya.

Tauraron zai rika dakon masu bincike zuwa sararin samaniya
Tauraron zai rika dakon masu bincike zuwa sararin samaniya REUTERS - JOE SKIPPER
Talla

Kasashen uku wadanda su ne mafi karfin tattalin arziki a yankin Turai, sun ce a cikin shekaru uku masu zuwa za su samar wa Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta yankin da kudaden da yawansu ya zarta Dala bilyan 3 da milyan 200 domin tafiyar da wannan aiki.

A karkashin shirin ne za a kera tauraron dan adam na zamani da zai rika dakon masu bincike zuwa sararin samaniya wanda aka yi wa take Ariane 6 da kuma Vega-C da ke matsayin cibiyar da ke kula da harba wannan tauraro.

A taron da suka fara jiya Talata, ministocin kula da sararin samaniya daga kasashe 22 na yankin na Turai, sun bayyana  cewa akwai bukatar zuba makudan kudade domin tafiyar da wannan gagarumin aiki, lura da cewa mafi yawan lokuta kasashen sun fi dogara ne da cibiyar SpaceX don gudanar da bincike-bincikensu.

Da farko dai kasashen na Turai sun tsara kaddamar da wannan tauraro da ake kira Ariane 6 ne tun a shekara ta 2020, to amma Daniel Neuenschwander, daraktan hukumar ta ESA da ke kula da ayyukan saman-jannati a yankin Turai, ya ce ba makawa aikin zai kankama a cikin shekara ta 2023 mai zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.