Isa ga babban shafi

An tallafa wa manoman Afrika da Asiya da Dala biliyan 1.4

Kananan manoma na kasashen Afrika da ke kudu da Sahara da na yankin kudancin Asiya, wadanda ke fama da radadin tasirin sauyin yanayi, sun samu tallafin Dala biliyan 1.4 domin tunkarar matsalar ta sauyin yanayi.

Wani bangare na taron sauyin yanayi na COP27 da ke gudana a Masar
Wani bangare na taron sauyin yanayi na COP27 da ke gudana a Masar AP - Peter Dejong
Talla

Tallafin kudin da ya fito daga Gidauniyar Bill da Melinda, za a rarraba shi ne cikin tsawon shekaru hudu, kuma an  ware shi domin gaggautaa bullo da kirkire-kirkiren tunkarar matsalolin sauyin yanayi da suka hada da fari da tsananin zafi da ambaliyar ruwa kamar yadda wata sanarwar taron sauyin yanayi na COP27 da ke gudana a wurin shakatawa na Sharm el-Sheikh na kasar Masar ta bayyana.

Mummunan yanayi ya lalata albarkatun gona a cikin wannan shekara, tare da rage yawan girbin da aka sabawa yi a nahiyoyi hudu na duniya.

Wasu kungiyoyi da ke wakiltar iyalai manoma har miliyan 350, sun mika wata budaddiyar wasika ga shugabannin duniya a yau Litinin, inda suke gargadin tsunduma cikin matsalar karancin abinci a duniya muddin gwamnatoci suka gaza wajen samar da kudaden bunkasa albarkatun gona ga kananan manoma.

Wasikar da kungiyoyin 70 suka yi tarayya wajen mika ta, ta ce, tsanantar yunwar da aka gani a bara, ta nuna raunin da ake da shi karara a fannin tsarin tattalin abinci a duniya da kuma rashin tanadin tunkarar tasirin sauyin yanayi.

Kungiyoyin da suka wakilci manoma da masunta da masu aikin gandun daji, sun ce,  dole ne wannan taron na COP27 ya muhimanta tsarin tattalin abinci da zai iya ciyar da wannan duniyar da ke dumama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.