Isa ga babban shafi

Mutane dubu 80 sun yi zanga-zanga a Jamus saboda mutuwar Amini

Kimanin mutane dubu 80 ne suka shiga zanga-zanga a birnin Berlin na kasar Jamus domin nuna goyon bayansu ga matan da ke gudanar da zanga-zanga a Iran saboda nuna bacin rai kan mutuwar Mahsa Amini wadda ta rasa ranta a hannun jami'an 'yan sanda a birnin Tehran.

Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da mutuwar Amini.
Wani bangare na masu zanga-zangar adawa da mutuwar Amini. AP - Markus Schreiber
Talla

Ministar Kula da Iyalai ta Jamus, Lisa Paus ta bayyana a shafinta na Twitter cewa, a yau dubban mutane na nuna goyon bayansu ga jajirtattun mata da ke zanga-zanga a Iran.

Wasu daga cikin masu tattakin a Berlin sun yi ta daga alluna masu dauke da kalmomi irinsu 'mata, rayuwa, 'yanci, yayin da kuma wasu ke ta nuna tutocin Kurdawa.

Jami'an 'yan sandan Jamus sun yi wa masu zanga-zangar rakiya, inda suka yi ta shawagi a kansau a cikin jirage masu saukar ungulu.

Kimanin makwanni shida kenan da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a Iran, inda a yau Asabar, hatta masu shaguna da ma'aikatan kamfanoni suka shiga yajin aiki a daidai lokacin da 'yan kasar ke ci gaba da nuna bacin rai kan mutuwar Amini mai shekaru 22, wadda 'yan sanda suka kama ta saboda karya dokar sanya hijabi, sannan daga bisani ta mutu a hannunsu.

Zanga-zangar dai ita ce mafi girma da aka gani a kasar Musulunci ta Iran a cikin tsawon shekaru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.