Isa ga babban shafi

Amurka da shugabannin EU sun taya Meloni murna

Shugabar Hukumar Kungiyar Kasashen Turai, Ursula von der Leyen ta taya sabuwar firaministar Italiya mai ra'ayin rikau, Giorgia Meloni murnar darewa kan karagar mulki, yayin da ta yi fatan samun kwakkwaran hadin-kai daga gwamnatinta.

Giorgia Meloni
Giorgia Meloni REUTERS - GUGLIELMO MANGIAPANE
Talla

Von der Leyen ta aika sakon taya murnar ne a shafinta na Twitter, inda ta ce, 

Ina taya Giorgia Meloni murnar zama firaministar Italiya, mace ta farko da  ta dare kan kujerar.

Kazalika shugaban Majalisar Tarayyar Turai, Charles Michel, shi ma ya yi lale marhabin da Meloni a matsayin sabuwar firaminista, inda ya bukace ta da ta bari su yi aiki tare domin ci gaban Italiya da kasashen Turai baki daya.

Har wa yau, mai magana da yawun Majalisar Dokokin Turai, Roberta Metsola, ita ma ta kambama sakonta na fatan alheri ga sabuwar firaministar, tana mai cewa, kasashen Turai na bukatar aiki tare da Italiya. 

Shi ma shugaban Amurka Joe Biden, ya taya sabuwar firaministar murna, inda ya ce, Italiya aminiyar kwarai ce ga Kungiyar Tsaro ta NATO, sannan kuma abokiyar kut da kut ce, yayin da ya yi fatan samun hadin-kai wajen ci gaba da bai wa Ukraine goyon baya tare da zargin Rasha da aikata laifin farmaki.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne, aka ayyana Meloni mai shekaru 45 a matsayin sabuwar firaministar Italiya, inda ta karbi ragamar jagorancin kasar wadda ita ce ta uku mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.