An tabbatar da Meloni a matsayin Firaministar Italiya
An tabbatar da shugabar masu ra'ayin rikau Giorgia Meloni a matsayin Firaministan Italiya bayan nasarar da jam'iyyarta ta samu a wani zabe mai cike da tarihi, inda ta zama mace ta farko da ta shugabanci gwamnati a Italiya.
Wallafawa ranar:
Bayan shafe kwanaki biyu ana tattaunawa tsakanin jam'iyyu, 'yar shekaru 45 da haihuwa daga Roma a yanzu ta tabbata cewa za ta kafa gwamnati hakan ya sanya ta kasancewa mace ta farko da ta zama Firaminista a tarihin kasar Italiya.
"A shirye muke mu baiwa Italiya gwamnati wacce za ta fuskanci matsaloli da suka addabe ta cikin gaggawa tare da wayar da kan jama'a muhimmancin ci gaban kasarmu," in ji Meloni.
Kasancewarta Firaministan ya kasance wani muhimmin abu ga kasar ta uku mafi karfin tattalin arzikin a kasashe masu amfani da kudin Euro.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu